Masu bikin Mauludi sun kasu kashi kashi.
1-masu yi da manufa mai kyau, su sukan yi shi kamar yadda Aka kirkire shi a Daular fadimiyya, wadannan ba su cika aikata Shirka da Fasadi a bikin na su ba, ba sa wuce cin abinci da karanta tarihin haifuwar Annabi saw da wakokin yabon sa, duk da wasu wakokin akwai wuce iyaka da bashi matsayin Mahalicci da kuma kissosi marasa inganci.
2-Wadan da suka maida bikin hanyar samun kudi da nuna karfin su da yawan mabiyan su,kamar wasu shehunan Dariqu da makusantan su, da suke rubutu wa Gomnatoti su basu kudi da kuma gudummawar mabiya garuruwa da kauyuka.
3- wadan da suke yi dan bada haushi wa wadan da suke ganin a bin a matsayin bid'a da musulunci ba ya so.
4- wadan da suke anfani da shi wajen kwaso mabiya daga wata tafiya zuwa ta su kamar Shi'a.
5-yan tamore tunda akwai gangwajewa da chashewa sheke aya samari da yan mata,
To cikin wadannan wa kake ga zai kubuta ?
Allah ka tabbatar da mu akan tafarki madaidaici, ka raya mu ka kashe mu akan Koyarwa da Soyayya da biyayya wa Annabi Muhammad saw.
No comments:
Post a Comment