Wednesday, December 14, 2016

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE

1.Ta rike masa amana 2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon Allah bane. 3. Ta kula da dukiyarsa 4. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman lafiya 5. TA girmama shi a gaban idansa 6. TA kare girmansa a bayan idansa 7. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a wajenta 8. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane awajenta 9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi. 10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga gareshi 11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi . 12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi 13.Idan ya bata kadan taga yawansa 14.Idan ya bata da yawa tayi godiya 15.Ta farka daga bacci kafin ya farka 16.Sai yayi bacci kafin tayi 17.Tayi hakuri idan yayi fushi 18 Tayi taushi idan yayi tsauri 19.Ta lallashe shi idan ya hasala 20.kada ta nuna raki a gabansa 21.kada tayi kuka alhali yana dariya 22.kada tayi dariya alhali yana kuka 23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu 24.kada ta matsa masa da bukatu 25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida 26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai 27.kada ta dinka kushe tsarinsa 28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta 29.Ta dinka girmama shi a wajen kawayenta 30.Ta dinka nuna masa abu mai kyau 31.Ta dinka boye abu mummuna 32.Idan ya kawo wata damuwa gareta, ta taimake shi ya warware ta 33.Idan ya nuna baya son wani abu ta daina 34.Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa 35.Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki 36.Ta tsaya da jinyar sa idan yana rashin lafiya 37.Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako 38.Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatu 39.Tayi masa rakiya lokacin fita ta tareshi a lokacin da ya dawo 40.Ta tausasa harshe a lokacin da take magana dashi 41.Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta 42.Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge 43.Tayi masa bankwana a lokacin balaguro 44.Tayi ado karshen iyawarta 45.Ta bayyana halaye masu kyau 46.Ishara ta ishi mai hankali ta kula wannan sosai 47.Ta bayyana kanta a matsayin mace 48.Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai 49.Ta cika zuciyarsa da sonta idansa da kwalliyarta 50.Tayi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so 51.Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata mummuna 52.Ta yafe masa idan ya munana mata 53.Ta karbi uzurinsa 54.kada tayi sallar nafila sai ta sanar masa 55.kada ta dau azumi sai ya sani. 56.kada ta fita daga gida sai ya sani. 57.Ta iya girki kala-kala. 58.kazantar jiki ta dade tana kashe aure a kula. 59.kada ta shigar da wani gidansa sai da izni. 60.kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai Allah ya zaunar damu lafiya da iyalan mu.

No comments:

Post a Comment